JAMUS TA CE ZA TA IZA WUTA WAJEN GANIN AN KARE HAKKIN DAN ADAM A DUNIYA. | Siyasa | DW | 29.07.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

JAMUS TA CE ZA TA IZA WUTA WAJEN GANIN AN KARE HAKKIN DAN ADAM A DUNIYA.

Ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta gabatad da shirye-shiryen da ma'aikatarta ta sanya a gaba na wanzad da manufofin gwamnatin tarayya kan kare hakkin bil'adama a duniya baki daya.

HEIDEMARIE WIECZOREK-ZEUL, ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus.

HEIDEMARIE WIECZOREK-ZEUL, ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus.

Da take gabatad da shirin, ministan ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayyar Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta ce Jamus ba za ta yi zaman `yan ba ruwanmu ba, tana ta kallon yadda a ko yaushe ake ta take hakkin bil’Adama a duniya baki daya, inda ta hanyar cin zarafin al’ummomi shugabannin kasashe da dama ke hana jama’a samun isashen abinci, da ruwa mai tsabta, da hanyoyin ilimantad da yaransu, da kuma yi wa mata danniya a wasu wuraren.

Don ganin cewa an kawo karshen wadannan ababan da ta lassafta, ministan ta ce ma’aikatarta za ta ba da karfi ne a sabbin manufofin da tsara, wajen karfafa wa kafofin kare hakkin dan Adam gwiwa a kasashe masu tasowa. Ta kuma ce a shirye gwamnatin Jamus take, ta tallafa wa kungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, wajen kafa kotun kula da batutuwan da suka shafi keta hakkin dan Adam a nahiyar. Ban da haka ma ministan ta kara da cewa.-

"A fannonin tattalin arziki, da na jin dadin zaman jama’a da al’adu da kuma shari’a, za mu ba da gudummuwarmu wajen ganin cewa ana da kafofin sa ido, wadanda aikinsu zai kasance, tabbatad da aiwatad da duk manufofin da za a tsara game da wadannan fannonin. A nan kuwa, kungiyoyin sa kai ma, za su iya taka muhimmiyar rawarr gani."

Abin da gwamnatin Jamus za ta fi ba da fiffiko a kai shi ne ganin cewa, an tabbatar wa kowa `yancin samun abinci, inji ministan. A nata ganin dai, yunwa da rashin samun ingantaccen abbinci mai gina jiki, wato ba matsala ce da ke da asali daga rashin noman abinci kadai ba. A zahiri ma, masu mulki a kasashe masu tasowan ne ba sa kula sosai da wannan fannin na noma da samad da isashen abinci, abin da kuma ke janyo sakamakon yunwa da fatara.

Ministan ta ci gaba da bayyana cewa, ma’aikatarta ta cim ma yarjejeniya da kasashe masdu tasowa fiye da 30, wadanda suka mince su bunkasa kafofin dimukradiyya, da inganta halin rayuwar jama’a da kuma bayyana duk wasu harkokin kasafin kudi da kuma yadda aka kashe kudade a kan ayyukan da aka aiwatar. Jamus dai ta kara yawan kudin da ta ware don cim ma wannan gurin, daga Euro miliyan 80, zuwa Euro miliyan dari 2 da 20.

Bunkasa ilimi kuma na da muhimmanci a tsarin manufofin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba, inji ministan. A nan dai za fi ba da karfi ne, wajen tallafa wa kafofin bai wa mata ilimi a kasashe masu tasowa. Ta yin la’akari da wani rahoton da aka buga a shekara ta 2002, kan ci gaban halin rayuwar jama’a a kasashen Larabawa, ministan ta ce an gano cewa, take hakkin mata a wadannan kasashen na cikin dalilan da ke janyo musu koma baya. A nan ma Jamus, a shirye take ta ba da tata gudummuwa:-

"Muna goyon bayan kafofin da ke yunkuri a yankin na kasashen Larabawa, wajen ilimintad da `yan mata, saboda ko wane mahaluki na da `yancin samun ilimi, kamar dai yadda gamayyar kasa da kasa ta yarje a kai."

Take wa mata hakikinsu dai, wata babbar illa ce da ya kamata a yake ta ala kulli halin, inji Heidemarie Wieczorek-Zeul. Ta kuma yi Allah wadai da abin da ta kira, danniyar da ake ta nuna wa mata, da fyade da ake yi musu a yankin Darfur na kasar Sudan, inda ta ce wannan wato aikata miyagun laifufukan yaki ne da kuma take hakkin dan Adam. Kamata ya yi dai a hukuntad da duk masu gudanad da wannan danyen aikin a kann mata, inji m inistan. Ta dai yi kira ga kafa wani kwamiti na musamman don ya binciki wannan batun, sa’annan kuma idan an tabbatar da gaskiyarsa, a gabatad da duk wadanda ke da hannu a ciki gaban shari’a.

Gwamnatin Jamus dai, ta kara yawan kudin da ta ware don taimaka wa `yan gudun hijira da ke ta fama da matsaloli daban-daban a kasar Sudan, musamman ma dai a yankin na Darfur. A halin yanzu kudin da aka ware don gudanad da aikin tallafa wa `yan gudun hijiran ya tashi zuwa Euro miliyan 33 da digo 5 inji ministan.

 • Kwanan wata 29.07.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvhg
 • Kwanan wata 29.07.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvhg