A ranar 9 ga watan Nuwamban 1989 katangar Berlin ta fadi, miliyoyin Jamusawa sun fantsama kan tituna cikin farin ciki. A ranar 3 ga watan Oktoban 1990 aka yi bikin sake hadewar Jamus ta Gabas da ta Yamma.
Miliyoyin Jamusawa daga yankin Gabaci da Yammaci sun fantsama kan tituna cikin farin ciki sakamakon faduwar katangar Berlin a ranar 9 ga watan Nuwamban 1989. Har yanzu akwai bambancin karfin tattalin arziki da ci-gaban kasa tsakanin yankunan biyu, shekaru 30 baya.