UN (MDD) Majalisar Dinkin Duniya ta kasance hukuma ta kasashen duniya wadda take kula da kare rikici tsakanin kasashen da kawo hadin kai.
An kafa majalisar a shekarar 1945 bayan yakin duniya na biyu. Majalisar wadda take da mazauni a birnin New York na Amirka, ta kunshi kasashe 193 kuma babban aikin da ta saka a gaba shi ne kare sake samun yaki a duniya.