Jam'iyyar Die Linke guda ce daga cikin jam'iyyun da ake da su a tarayyar Jamus kuma ta na daga cikin wanda ke da karfin fada a ji duba da irin rawar da ta ke takawa a fagen siyasar kasar.
Yankunan da jam'iyyar ke da karfi na zama sabbin jihohin Jamus a tsohuwar Jamus ta Gabas. Ana iya cewa na da tsohon tarihi domin ana ganin ta samo asali daga jam'iyyar 'yan gurguzu ta Socialist Unity Party (SED) wacce ta mulki Jamus ta Gabas GDR har sai lokacin da aka hade Jamus ta Gabas da Jamus ta Yamma a shekarar 1990.