Jamus ta kuduri aniyar ba wa Kurdawa makamai | Siyasa | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta kuduri aniyar ba wa Kurdawa makamai

Gwamnatin tarayyar Jamus ta fara nazari kan irin makaman kasar da za ta iya ba wa mayakan Kurdawa a fafatawar da suke yi da 'yan IS a Iraki.

Gwamnatin kasar ta Jamus dai ta umarci kwararrunta da su gudanar da bincike irin tallafin da za a iya bai wa Kurdawan Iraki bisa yakin da suke yi da 'yan ta'adda wadanda ke ikirarin yin Jihadi a arewacin Iraki.

Da farko dai gwamnatin tarayyar Jamus ta yi ta nunan taka-tsantsan bisa rikicin da ke faruwa a Irakin, to amma ganin yadda 'yan ta'addan ke kara samun karfi, hakan ya sa mahukunta a Berlin sun sauya tunani kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana.

"Wadannan makamai da za mu tura Iraki, manufar tura su ita ce, a karfafa wa damarar jami'an tsaron Kurdawan arewacin Iraki, ta yadda za su kare kansu daga mayakan ISIS."

To sai dai fa babbar jam'iyyar adawa ta SPD wanda Steinmeier ke ciki tana adawa da wannan mataki. Domin a tsarin jam'iyyar ana adawa da tura makamai wuraren da ake yaki. Amma ministan na harkokin wajen Jamus din ya kare wannan matakin, inda ya ce abinda ke faruwa a Iraki wani lamari ne dabam.

Rashin farin jinin tura makamai

Pressekonferenzzu Waffenlieferungen an irakische Kurden

Ursula von der Leyen da Frank-Walter Steinmeier

Ita jam'iyyar adawa mai manufar kare muhalli ta The Greens ta nuna rashin amincewarta. Don haka sun bukaci gwamnati ta yi wa majalisar dokoki bayani kan manufar tura makaman. Kathrin Görin Eckerhardt jagoran jam'iyyar a majalisar tarayya ta ce.

"Tura wasu makamai na yaki, kamar su rokoki da motocin sulke, wadannan idan gwamnati na san yin haka, to dole sai hakan ba zai yiwu ba tare da amincewar majalisar dokokin tarayya."

Ita kuwa jam'iyyar Die Linke, cewa ta yi kwata-kwata batun tura makamai ba mafita ba ce ga rikicin, duk da cewa an san ceton jama'a ake son yi, kamar yadda kwararre a jam'iyyar Jan van Aken ke cewa.

"Na fahimta cewa lallai akwai muhimmanci a taimaka wa Kurdawa. Mutane na mutuwa a yankin domin ba su da wadataccen abinci, ba su da magungunan kiwon lafiya. Amma a ce wai mu aika musu makaman yaki, wannan muguwar dabara ce, hakan yana nufin a kara kashe mutanen kenan."

'Yan IS a Iraki barazana ce ga Turai

Propagandabild IS-Kämpfer

Hoton farfaganda na mayakan IS

To amma da take jawabi ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta kare matakin, inda ta ce ganin mummunan aikin da 'yan ta'adda ke aikatawa a Iraki, idan aka bar su suka ci gaba da samun gindin zama, to wata babbar barazana ce ga kasar Jamus kanta.

Nan da ranar Laraba mai zuwa ne dai gwamnatin Jamus za ta yanke shawara ko irin wadannan makamai za ta iya aika wa Kurdawan arewacin Iraki. Baya ga kasar Jamus dai, akwai kasashen Turai kamar su Birtaaniya, Italiya da Faransa wadanda su ma suka bayyana shirinsu na tallafa wa Kurdawan Iraki da makamai a yakin da suke yi da 'yan ta'adda da ke cewa za su kafa daular Islama.

Mawallafa: Heiner Kiesel / Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin