Zaben jihohin Jamus ya ba da mamaki | Siyasa | DW | 15.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben jihohin Jamus ya ba da mamaki

Kasa da shekara guda da girka ta, Jam'iyyar masu adawa da manufofin Turai ta AfD ta fara nuna alamun kasancewa babbar barazana ga manyan jam'iyyun kasar nan gaba.

A nan Jamus, jam'iyyar AfD wadda ke adawa da manufofin Turai, wadda kuma ta ke kiran kanta zabi wa Jamus ta lashe zabukan da aka yi a wasu biranen yankin gabashin kasar a karshen makon da ya gabata, bayan da ta sami yawan kuri'un da ya zarta kashi goma cikin 100.

A wannan litinin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta karyata duk wani zargi na cewa za su kwaskware jam'iyyarsu ta yi la'akari da mahimman manufofin masu ra'ayin mazan jiya a jam'iyyarta, a wani mataki na kawar da kalubalen da suke fiskanta daga jam'iyyar AfD ta masu adawa da manufofin Turai, bayan da suka baiwa kowa mamaki a karshen zaben na karshen mako, inda ta ce bisa la'akari da sakamakon da suka samu a zabukan da aka yi a matakin Tarayya, da kuma kuri'ar jin ra'ayin jama'a babu wata bukatar su hassala.

Girkuwar jam'iyyar da samun karbuwar wajen al'umma

A shekara ta 2013 aka girka wannan jam'iyya ta AfD domin ta kalubalanci kudaden ceton da aka rika baiwa kasashen Turan da suka yi fama da karayar arziki, amma kuma ta sha suka sosai daga sauran jam'iyyun kasar wadanda suka ce tana da matsanancin ra'ayin rikau kuma tana da alaka da masu ra'ayin 'yan Nazi wato jam'iyyar NPD.

Parteitag Alternative für Deutschland (AfD) in Erfurt 23.3.2014

Jam'iyyar AfD ta karyata hasashen da aka yi

Sai dai kuma, sakamakon zabukan da aka yi bayan kafa ta, ya nuna cewa tana samun magoya baya ne daga kusan dukka jam'iyyun kasar. Idan har jam'iyya ta dauke matsayin mai matsakaicin ra'ayin rikau, to ko za ta kasance babban kalubale ga jam'iyya mai mulki ta CDU domin akwai wadansu daga cikin manufofinsu da ke kama, to sai dai jam'iyyar ta ce ko daya ba ta da niyyar yin kawance da ita.

Merkel ta hakikance kan cewa zabukan da aka yi na gama gari wanda ya baiwa jam'iyyarta nasara, ya nuna cewa kasa na amanna da manufofita to sai dai jami'yyar SPD na masu ra'ayin gurguzu ta ce ba zata sake yin kawance da ita ba bayan zaben shekara ta 2017 wanda ke nufin ke nan watakila sai ta lashe amanta ta koma ta nemi yin kawance da jam'iyyar ta AfD.

Sauti da bidiyo akan labarin