Christian Social Union (CSU) jam'iyya ce da ke da karfinta a jihar Bavaria da ke kudancin Tarayyar Jamus.
Jama'yiyyar CSU da ke da ra'ayin mazan jiya na kawance da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. Galibin mambobin jam'iyyar mazauna karkara ne.