Merkel ta yi kiran a zaba wa Jamus makoma | Labarai | DW | 24.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yi kiran a zaba wa Jamus makoma

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bukaci a zabi wanda take son ya gaje ta, a daidai lokacin da aski ya zo gaban goshi dangane da zaben kasa na ranar Lahadi.

Angela Merkel ta ce akwai bukatar a zabi Armin Laschet, mutumin da take muradin ya gaje ta domin Jamus ta ci gaba da kasancewa a bisa gwadaben ci gaba da take kai a yanzu.

Wannan kira na Angela Merkel ya ci karo da lokacin da dubban matasa masu fafutukar kare muhalli karkashin jagorancin matashiyar nan 'yar kasar Sweden, Greta Thunberg, ke zagaya manyan biranen Jamus.

Matasan dai na kiraye-kiraye ne gama da kawo sauyi da kuma sauya dabaru masu nasaba da kare muhalli.

A yayin jan hankalin da take yi wa galibi tsoffin masu zabe, Angela Merkel ta ce babu mafita da ta wuce Jamus ta ci gaba da shugabnni daga jam'iyyun CDU da CSU.