Shirin kafa gwamnatin kawance a Jamus | Siyasa | DW | 30.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin kafa gwamnatin kawance a Jamus

Bayan kammala zaben 'yan majalisu a Jamus, yamzu abin da ya rage shi ne kafa gwamnati. Manyan jam'iyyu biyu da suka samu rinjaye, wato SPd da ke zaman kan gaba da kuma CDU ta Angela Merkel na zawarcin sauran jam'iyyu.

Symbolbild Abschied der Bundeskanzlerin Angela Merkel NEU

Jam'iyyun SPD da CDU zawarcin jam'iyyun kafa gwamnatin da za ta gaji Angela Merkel

Su dai jam'iyyun na SPD da CDU da abokiyar tagwaiotakarta ta CSU, sun kasance a matsayi na daya da na biyu a zaben 'yan majalisar dokokin ta Jamus wato Bundestag. Jam'iyyar SPD ce dai ke kan gaba yayin da CDU/CSU din ke bi mata a ,matsayi na biyu. Jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli ce a matsyi na uku yayin da ita kuma jam'iyyar FDP ke a matsayi na hudu. 

Yayin da jam'iyyar SPD ta shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke kan gaba a zaben, ke zawarcin jam'iyyun biyu domin kafa gwamnatin hadaka, a hannu guda jam'iyyar CDU/CSU ta shugabar gwamnati mai barin gado Angela Merkel ta bayyana cewa ita ma fa za ta iya kafa gwamnatin hadaka, inda itan ma ke zawarcin wadannan jam'iyyu biyu na The Greens da kuma FDP. Wanna dai shi ne karon farko a tsayon shekaru da gwamnatin hadakar ka iya kunsar jam'iyyu sabon zubi, maimakon SPD da C DU/CSU da aka saba da su.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin