Wanene Olaf Scholz da ya ceto jam'iyyar SPD? | BATUTUWA | DW | 27.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Wanene Olaf Scholz da ya ceto jam'iyyar SPD?

Wai shin wane ne dan siyasar nan da ya farfado da jam'iyyar SPD, har ya kai ta ga samun mafi rinjayen kuri'u a zaben 'yan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag?

Deutschland | Nach der Bundestagswahl - SPD

Dan takarar kujerar shugaban gwamnatin Jamus na jam'iyyar SPD Olaf Scholz

A yayin yakin neman zabe da aka gudanar, jam'iyyar SPD ta dogara kan dan takararta a mukamin shugaban gwamnati Olaf Scholz wajen cimma burinta. Hotunansa ne suka mamaye allunan yakin neman zabe, sannan shi ne ke ruwa da tsaki a muhawarar siyasa da ake shiryawa. Sakon da SPD ta nemi isar wa shi ne: Gwaninta mai shekaru 63 wani jajirtacce ne da zai iya tafiyar da gwamnati ba tare da wahala ba. Ma'ana ya cancanci maye gurbin Angela Merkel da ba ta tsaya takara bayan shekaru 16 na mulkin Jamus ba. Scholz ya kasance ministan kudi a gwamnatin Merkel tun daga shekarar 2018, sannan ya kasance mataimakin shugabar gwamnati a kawancen gwamnatin CDU da abokiyar tagwaitakarta CSU da kuma SPD. Hasali ma zai ci gaba da rike mukaminsa har lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati. Scholz ya kasance dan takara na jam'iyyar da ya gaza zama shugabanta, a lokacin da aka gudanar da babban taro na kasa.

Karin Bayani: Kyakkyawar alakar Jamus da Afirka na da tarihi

A shekarar 2019 ne Olaf Scholz ya so zama shugaban jam'iyyar SPD, amma ya sha kashi a hannun Saskia Esken da Norbert Walter-Borjans wadanda suka yi alkawarin kyautata manufofin jam'iyyar a siyasance. Olaf Scholz ya kasance a bangaren masu ra'ayin mazan jiya na SPD. Sai dai abin da ya fi ba da mamaki shi ne, nadinsa a matsayin dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus bayan zaben 'yan majalisu a watan Agusta na 2020. Tun daga wannan lokaci ne Scholz ya yi alkawarin yin aiki tukuru, wajen mayar da jam'iyyar tsintsiya madaurinki daya: "Abin sani a nan shi ne, mun samu hanyar yin aikin hadin gwiwa kuma cikin jituwa da hadin kai har ma da tausayawa. A zahiri mun fara yin aiki tare da juna kai tsaye bayan zaben shugaban SPD, kuma akwai yarda da juna tsakaninmu, don haka a wani lokaci tabbas na ji cewa su shugabannin biyu za su yanke shawara, kuma dukkansu suna da kyakkyawar niyyar cewa za su bani takara."

Tsarin zaben Jamus tsari ne mai sarkakiya sosai, amma kuma akwai dalilai kwarara da suka sanya hakan

Olaf Scholz dai, mutum ne mai karfin hali da rashin damuwa duk da kalubalen da yake fuskanta. A cikin shekarun da ya shafe a fagen siyasar Jamus ya gamu da wasu matsaloli, amma ba su sa shi kaucewa alkiblar da ya sa a gaba ba. Ko da abin kunya a harkar haraji na Cum-Ex da badakalar zamba ta Wirecard da suka sa Scholz gurfana a gaban kwamitocin bincike na majalisar dokokin Jamus, ba su haifar masa da wata illa a fannin siyasa ba. A lokacin da annobar corona ta barke ma dai, Scholz a matsayinsa na ministan kudi na Jamus ya yi amfani da wannan dama wajen shan romon irin tallafin da ma'aikatarsa ta bayar. Hasali ma dai, Jamus za ta karbi sabon bashin Euro biliyan 400 kafin karshen shekara ta 2022.

Karin Bayani: Gwamnatin Merkel na cikin rudani

Scholz ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewar kasar za ta iya biyan wannan bashin cikin hanzari: "Wannan basuka ne wanda muke yin abin da ya zama dole mu yi yanzu. Za mu yi amfani da duk wata hanyar da ta samu, kuma mu tabbatar da cewa za mu iya tsallake wannan mawuyacin lokaci tare da dogaro kan damar tattalin arzikinmu da kuma tabbatar da cewa mun fita daga halin da ake ciki."

Deutschland Bundestagswahl 2021, SPD feiert die Sieger

Jam'iyyar SPD na murnar samun rinjaye, a zaben majalisar dokokin Jamus ta Bundestag

Scholz ya yi makamancin wannan alkawarin a fannin yaki da sauyin yanayi. Da ma ya dade yana fadar cewa 'yan jam'iyyar The Greens na da kyawawan manufofi a fannin kare muhalli, amma ana iya aiwatar da su ne kawai karkashin hadin gwiwa da jam'iyyarsu ta SPD domin ya yi tasiri a fuskar tattalin arziki da zamantakewa. Dangane da manufofin kasashen waje kuwa, yana son dorawa ne inda Merkel ta tsaya, inda ya ce a karkashin jagorancinsa Jamus za ta yi aiki domin samar da "Turai mai karfin fada a ji, wacce kuma za ta rinka magana da murya daya, saboda in ba haka ba nahiyar za ta samu koma baya. Olaf Scholz ya ce zai hada gwiwa da Amirka, musamman ma a wannan yanayi da duniya ta samu kanta a ciki. Wannan matakin dai, ya hada da aiki tare a cikin kungiyar tsaro ta NATO. A bayyane yake cewa, wannan manufa ta sami karbuwa sosai ga al'ummar Jamus.

Sauti da bidiyo akan labarin