SPD da aka kafa a 1875 ita ce jam'iyyar da ta fi dadewa da kafuwa a Jamus. Ta samu tushenta a karni na 19 lokacin gagwarmayar 'yan kodago.
Ita ce ta biyu a farin jini idan aka yi la'akari da yawan kuri'un da take samu a zabuka, amma ta daya a yawan magoya baya. Ta fi samun karbuwa tsakanin ma'aikatan manyan birane da ke da karamin karfi.