Jam'iyyar the Green na daya daga cikin jam'iyyun mafi girma a Jamus. An gina jam'iyyar ce kan manufa ta kare muhalli a kasar
The Greens ta dogara ne ga wayayyu 'yan boko, mafi akasari a birane don haka ta ke da muradi na mamaya a manyan birane na Yammacin Jamus musamman a yankunan da ake da jami'o'i. Jam'iyyar yanzu haka na daga cikin wanda ke da wakilci a majalisar dokokin kasar ta Bundestag.