1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kawancen jam'iyyun Jamus ya amince da kafa gwamnati

December 7, 2021

Kawancen jam'iyyun siyasar Jamus na SPD da The Greens da FDP ya rattaba hannu kan kafa sabuwar gwamnati a wannan Talata a birnin Berlin, kwana daya kafin rantsar da sabon shugaban gwamnati a gobe Laraba. 

https://p.dw.com/p/43wQj
Deutschland | PK Olaf Scholz
Hoto: Markus Schreiber/AP Photo/picture alliance


Yarjejeniyar na zama mataki na karshe kafin ranar Laraba, inda Majalisar Dokoki ta Bundestag za ta tabbatar da Olaf Scholz na jam'iyyar SPD a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus a hukumance, matakin da zai kawo karshen wa'adin shugabancin Angela Merkel na tsawon shekatru 16. 

Jagorar jam'iyyar The Greens  Annalena Baerbock  wace ta samu mukamin ministan harkokin wajen Jamus da jagoran jam'iyyar FDP Christian Lindner da shi kuma ya samu mukamin ministan kudi, sun jinjina wa hadin kan da suka samu daga jam'iyyar SPD wace ke da kaso mai tsako a sabuwar gwamnatin ta Jamus.