Jamus kasa ce da ke nahiyar Turai kuma ita ce ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a nahiyar.
Tarayyar Jamus na daga cikin kasashen da ke da karfin fada a ji a duniya kuma ta zaman daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen kere-kere musamman ma abinda ya danganci motoci.