Jamus da Faransa na nazari kan tattalin arzikin Turai | Labarai | DW | 29.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Faransa na nazari kan tattalin arzikin Turai

Shugabannin kasashen Jamus da kuma Faransa na wata ganawar domin nazarin hanyoyi farfado da tattalin arzikin kasashen Turai sakamakon matsalolin da suka fuskanta saboda corona.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta fara wata ganawar da suka shirya yi da Emmaunel Macron na kasar Faransa domin nazarin hanyoyi farfado da tattalin arzikin kasashen Turai sakamakon lahanin da annobar corona ta yi musu.

Merkel ta karbi bakuncin Macron din ne a arewacin birnin Berlin, inda shugabannin biyu za su tattauana kwanaki biyu kafin Jamus ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar EU.

Dama akwai wani kasafi na musamman da aka tsara wa batun sake farfadowa daga masassarar coronar ta fuskar tattalin arziki da ta shafi kasashen, wanda ya kunshi kudaden da suka kai Euro biliyan 500, kwatankwacin dala biliyan 560.

Haka nan akwai wasu kudaden da suka ware na rance da su kuma suka kai Euro biliyanm 250.