Turai nahiya ce daga cikin nahiyoyin da muke da su a duniya.
Kasashen da suka yi fice a wannan nahiya ta Turai sun hada da Birtaniya wadda ta yi wa kasashen duniya da dama mulkin mallaka. Faransa da Italiya da Jamus na daga cikin kasashen da suka shahara a nahiyar.