1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU na neman dakile kwararar bakin haure daga Afirka

June 11, 2024

'Yan asalin Afirka da ke kokarin shiga Turai ba bisa ka’ida ba na ratsa teku bayan biyowa ta hamadar Sahara. Sai dai Kungiyar Tarayyar Turai na daukar matakan dakile wannan tunani, amma yanzu matasan na bi ta Moritaniya.

https://p.dw.com/p/4gvGb
Bakin hauren Afirka na fuskantar hadari a iyakar Tunisiya da kasashen Turai
Bakin hauren Afirka na fuskantar hadari a iyakar Tunisiya da kasashen TuraiHoto: Yousef Murad/AP/picture alliance

Matasan Afirka maza da mata na kama hanyoyi da ke cike da hadari a duk shekara domin ganin sun shiga cikin kasashen Turai. Sai dai galibinsu na shiga miyagun hannu ko kuma ta kai ga rasa rai a lokutan haduran kan ruwa, ko kuma saboda tsananin azaba da suke cin karo da su. 

Karin bayani:MSC: kalubalen kwararar bakin haure a duniya

Wata da ta bayyana sunanta a matsayin Lala da ta girma a Senegal da kasar Moritaniya ta taso da burin samun rayuwa mai inganci. Ta kwashi lokaci tana tsumin kudin biyan masu fito da kananan kwale-kwale da masu safarar mutane zuwa Turai ke amfani da su. Shi dan kwale-kwalen na daukar mutane daga birnin Nouakchott na kasar Moritaniya zuwa tsibirin Canary inda daga nan kuma suke kama hanyar zuwa Turai ta teku.

Bakin haure na kasadar ratsa teku don shiga Turai ta barauniyar hanya
Bakin haure na kasadar ratsa teku don shiga Turai ta barauniyar hanyaHoto: Dan Kitwood/Getty Images

Lala ta yi bayanin wahalar da sha a tafiyar da ta bi ta kasar Moritaniya, inda ta ce: " 'Yan kasashe da dama ne ke wannan tafiyar kasada da suka hada da 'yan Mali da Kamaru da Najeriya da Senegal da Moritaniya. ‘Yan sanda kan kai mutane bakin gada inda babban jirgi ke jiran ku a kan teku domin wucewa da ku zuwa Turai. Ba kowa ne yake samun shiga ba saboda yawan mutane ya zarta mutum 100. Daga ciki 80 ne suka shiga."

Karin bayani:Nijar: Bai wa bakin haure damar wucewa Turai

A tsakanin Janairu zuwa Maris na shekarar 2024, bakin haure dubu 12,293 ne suka shiga kasar Spaniya ta barauniyar hanyar. A bara dai a daidai wannan lokaci, baki dubu 2,178 ne suka shigo Turai ta tsibirin Canary bayan barin kasar Moritaniya. Wani masunci mai suna Ali ya nuna wasu hotuna mara dadi da ya dauka a gabar ruwa. Ya ce "dubi wani ne da ya mutu, gawarsa ce a nan. Wadannan ma gawarwakin ne, kai dubi wannan kam jariri ne a nan. Ba karamin sako ba ne wannan".

Shugabar hukumar zartaswa ta EU Ursula von der Leyen da shugaban Tunisiya Kais Saied
Shugabar hukumar zartaswa ta EU Ursula von der Leyen da shugaban Tunisiya Kais Saied Hoto: AFP

Matashiya Lala ta ce har yanzu tana fama da tashin hankalin da ta gani a tafiyar da ta yi, duk da cewa an tasa keyarta zuwa gida Moritaniya bayan cin karo da jam'ian tsaro. Ta ce: ''Tunda na dawo har yanzu ban iya barci ba. Don ko da na rufe idanuna, sai in ta ganin kamar ina cikin jirgin ruwan ne da ke tangal-tangal a cikin teku.''

Karin bayani:Nijar: Bakin haure na cikin tasku bayan juyin mulki

Cikin watan Afrilun da ya gabata, Kungiyar Tarayyar Turai ta bai wa Moritaniya tallafin Euro miliyan 210, inda miliyan 60 daga ciki take son a yi amfani da su wajen yaki da harkokin safarar bakin haure zuwa kasashen Turai. EU na kokarin shiga yarjejeniya da kasashen wadanda a baya suka taimaka wajen dakatar da kwararar bakin haure da ke bin barauniyar hanya.