1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure na cikin tasku bayan juyin mulki

Vincent Niebede AH, MAB
August 17, 2023

Halin da bakin haure ke ciki a Nijar na kara tabarbarewa bayan juyin mulkin sojoji, sakamakon yadda Kungiyar Tarrayar Turai ta dakatar da yarjejeniyar yaki da kwararar masu neman tsallakawaTurai ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/4VHgW
Bakin hauren Nijar na cikin tasku bayan juyin mulki da sojoji suka yi a kasar
Bakin hauren Nijar na cikin tasku bayan juyin mulki da sojoji suka yi a kasarHoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Akwai adadin mafi girma na bakin haure da ke rarrabe a cikin cibiyoyi bakwai a Nijar, wadanda ake daukar nauyinsu ta hanyar 'yan kudade da ake samu daga kungiyar EU. Akwai cibiyoyi hudu a Agadez yayin da ake da uku a yankin Yamai inda ake da tarin 'yan ci ranin. Amma dakatar da tattaunawar da aka yi tsakanin hukumomin Brussels da Yamai na haifar da matsala a sansanonin 'yan ci rani, a cewar reshen Nijar na Hukumar kaura ta MDD OIM.

Jami'an OIM na furicin cewar idan ba a samun dawowar farar hula a kan mulki ba, rayuwar bakin haure za ta shiga cikin wani mawuyacin hali sakamakon yadda kungiyar ta daina ba da agaji ga Nijar domin kula da bakin haure da ma tsayar da su zuwa nahiyar Turai

Abdoulaye Abderrahmane Amadou da ke shugabancin wata kungiya mai sunan Humanite a Nijar, ya ce: "Dakatar da taimakon da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi a Nijar na iya yin tasiri ga al'amuran ƙaura. Mai yiyuwa ne hatta matasan Nijar su yi hijira saboda dalilan tsaro saboda halin da ake ciki a kasar”.

Jihar Adagez ta zama matattarar bakin haure da ke neman zuwa Turai
Jihar Adagez ta zama matattarar bakin haure da ke neman zuwa TuraiHoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Tun a shekarar 2015 ne Nijar ta fara aiwatar da manufar rage yawan tudadar bakin haure wadanda akasarinsu ke bi ta Agadez kafin su isa Libiya domin tsallakawa zuwa nahiyar Turai. Ita dai Nijar ta rattaba hannu tsakaninta da Kungiyar Tarrayar Turai kan wata yarjejeniya da ke kara kaimi wajen yaki da bakin haure da ke hijira ba bisa ka’ida ba. Tana inganta iyakoki da bayar da dama ga wadanda ke rayuwa daga kaura a kasar don gudanar da wasu harkokin ta yadda za su yi watsi da ra'ayin zuwa Turai.

Emmanuel Dupuy, shugaba wata kungiya mai lura da sha'anin tsaro a Turai ya ce: "Kusan bakin haure 100,000 ne ke tsare a cikin sansanoni a Nijar maimakon ganin sun tsallaka zuwa Libiya sannan su tafi nahiyar Turai. A yanzu dai dakatarwar ce kungiyar EU ta yi a kan yarjejeniyar, amma babu wani hukunci a hukumance. Nan gaba ne a a ranar 30 ga watan Augusta a taron ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarrayar Turai za su bayyana ko za a ci gaba da shirin ko akasin haka."

Bisa ga dukkan alamu dai,  kungiyar EU ba za ta ci gaba da aiwatar da shirin ba, wanda a kowace shekara take zuba wa Nijar makudan kudade a kan batun yaki da kwarrarar bakin haure, saboda korafin da ta yi cewar sai hallastatun shugabannin kawai za ta iya yin aiki da su.

Migranten in Agadez
'Yan Senegal masu karancin shekaru na cikin masu bin Agadez don zuwa TuraiHoto: DW/K. Gänsler

Maria Arena da ke zama 'yar majalisar dokoki ta EU ta ce:  "Gwamnatocin masu mulkin kama karya na kara yawan kwararar bakin haure zuwa Tarayyar Turai.  Ba mu da tabbas a kan abin da muka cimma a kan yarjejeniyar kare 'yancin bakin haure kamar yadda yake faruwa a Tunisiya, abu ne da ka iya faruwa. A kan yarjejeniyar da muka kulla da Nijar, mu Majalisar Tarayyar Turai ba mu tantanceta ba  har ya zuwa yau, amma a ganina, abu mai muhimmanci shi ne a ci gaba da tattaunawa da Nijar kan ka'idojin kare hakkin dan Adam."