Majalisar Tarayyar Turai na da wakilai da ake zabe daga kasashen da ke cikin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.
Majalisar mai mambobi 766 na yin zamanta ne a birnin Brussels na kasar Beljiyam da kuma birnin Strasbourg na kasar Faransa. Majalisar har wa yau tana da ofisoshi a kasar Luxemburg.