1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ta leko ta koma wa masu kyamar baki a zaben Turai

June 10, 2024

Da gagarumar nasarar ce jam'iyyun da ke da tsattsaurar ra'ayin kyamar baki suka samu rinjaye a kasashe Faransa da Jamus a zaben 'yan majalisar dokokin Kungiyar Tarayyar Turai. Sai dai har yanzu jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayin rikau ne ke da rinjaye a majalisar dokokin ta EU.

https://p.dw.com/p/4gsEt

Sakamakon zaben majalisar dokokin EU ya nuna cewa har yanzu rukunin jam'iyyun European People's Party (EPP) na kan gaba a yawan 'yan majalisu. Wannan nasarar ta masu matsakaicin ra'ayi a zaben zai ba da dama ga shugabar hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai EU Ursula von der Leyen ta yin tazarce a wa'adi na biyu har zuwa shekarar 2029.

Shugabar ta bayyana nasarar da jam'iyyun da ke da ra'ayin rikau suka samu a matsayin gamsuwa da kamun ludayin shugabancinsu. Ta ce " Yau rana ce mai matukar mahimmanci ga rukunin jam'iyyun European People's Party (EPP), mun samu nasarar lashe zabe kuma mune har yanzu ke kan gaba, wannan na nuna cewar masu kada kuri'a sun gamsu da salon mulkinmu aZaben majalisar dokokin Turai na 2024 tsawon shekaru biyar. "

Karin bayani: Zaben majalisar dokokin Turai na 2024

Ursula von der Leyen za ta iya samun wa'adi a shugabancin hukumar EU
Ursula von der Leyen za ta iya samun wa'adi a shugabancin hukumar EUHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

 A makonni masu zuwa ne, von der Leyen za ta nemi goyon bayan kujerun majalisar 361 cikin 720 da ake da su a majalisar Turai, inda alamu suka nuna cewar za ta iya yin tazarce tunda  EPP da jami'iyyun masu matsakaicin ra'ayi da kuma jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi sun lashe lashe fiye da kujeru 400. 

Masu ra'ayin rikau sun samu nasara a Jamus

Sai dai jam'iyyun da ke kyamar baki sun samu rinjaye a wasu kasashe mambobin kungiyar. A nan Jamus, jam'iyyar mai tsattsauran ra'ayi ta AFD ta zo ta byiu a zaben, inda jam'iyyar Social Democrat da ke jagorancin jam'iyyun hadaka ta shugaban gwamnati Olaf Scholz ta samu koma baya. Ana alakanta hakan da yadda masu kada kuri'ar ke nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam'iyyun. A nasu bangaren, Kawance jam'iyyun CDU/CSU a Jamus na kan gaba a zaben.

Shugaban jam'iyyar CDU Friedrich Merz ya ce wannan babban sako ne ga shugaba Scholz, inda ya ce: " Wannan sakamako, tilas ne ya sanya gwamnatin tarayya ta sake nazari kuma dole ta sauya manufofinta. Akwai bukatar sauyi a salon siyasar Jamus, domin haka ne nake kira ga shugaban gwamnati da kawancen jam'iyyun social Democrat da masu rajin kare muhalli na The Greens da FDP cewar, lamura ba za su ci-gaba da kasancewa kamar yadda suke ba a shekaru biyu da rabi masu zuwa ba."

Jam'iyyar Macron ta sha kaye a Faransa

Marine Le Pen da Jordan Bardella ne jagororin jam'iyyar RN a Faransa
Marine Le Pen da Jordan Bardella ne jagororin jam'iyyar RN a FaransaHoto: Julien de Rosa/AFP

A Faransa, Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da rushe majalisar dokokin kasar, inda ya bukaci a gaggauta gudanar da sabon zabe bayan da  jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Marine Le Pen ta lallasa jam'iyarsa. 'Yan kasar irin su Nicolas Desurmount na cewa, wannan wata babbar dama ce ga gwamnatin Farasa ta sake sabon lalle.

Karin bayani:Majalisar dokokin EU ta cika shekaru 70 
 
Desurmont ya ce: " Ba kasafai ake ganin abun da ya faru a jiya ba, wannan wani gagarumin sako ne ga gwamnati, akwai matsaloli da dama da ake fuskanta da suka shafi bangarorin zamantakewa da muhalli da kuma ayyukan yi. A tunanina, kiran da gwamnati ta yi na a sake zabe a kasar zai bata dama da za ta samar wa kanta mafita a shekaru masu zuwa ba. "

Sai dai a Italiya, jam'iyyar Giorgia Meloni ta FDI ta samu gagarumar nasara. Yayin da a kasashen Sweden da Denmark da Finland, jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi da kuma masu rajin kare muhalli suka yi nasara.