Babban zabe a Najeriya na daukar hankalin duniya baki daya kasancewa kasar ta fi kowace kasa a Afirka yawan al'umma da aka kiyasta sun kai mutum miliyan 200, ita ce kuma babbar daula a Afirka ta Yamma.
Fannonin tsaro da yaki da cin hanci da tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 a tarayyar Najeriya. Saboda haka ne 'yan takara dabam-dabam ke kewayawa sako da lungu na kasar don tallata manufofinsu ga 'yan Najeriya da nufin samun kuri'unsu. DW ta shirya jerin rahotanni kan fannoni da dama a kan wannan zabe.