1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan adawa ga ICPC kan tsare El-Rufa'i

February 20, 2026

A yayin da tsohon gwamnan jihar kaduna Malam Nasiru El Rufa‘i ke shirin share daukacin mako yana bakuntar jami'in tsaron Najeriya, damuwa na dada girma daga 'yan adawa kan rawar jami'an tsaro a kokarin murde adawar

https://p.dw.com/p/59A8x
Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

El Rufa'in dai ya share kwanaki yana sauyin hannu a tsakanin jami'an hukumar EFCC da na ICPC da sunan bincike dwana 'yan adawa ke kallo a matsayin take hakki. 

Duk da cewar dai sun fake cikin bin ba'asi, ci gaba da kame tsohon gwamnan jihar kaduna Nasir El Rufa'i

da kuma samamen da aka kai gidansa da ke Abuja yana neman yamutsa hazo a tarayyar Najeriya.

Ko bayan share kwanaki biyu a hannun EFCC tsohon gwamnan ya shiga kwana na biyu a hannu na jami'an ICPC duk a cikin neman ba'asin kisan abun da ya kai Naira miliyan dubu 432 a zamanin mulkinsa.

Akwai ma yiwuwar sake rike shi a bangaren DSS da ke fadin yana da tambayoyin amsawa bisa kisan wani malami a Jami'ar Dutsinma.

Karin Bayani:El-Rufai ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo

Rundunar 'yan sandan Najeriya
Rundunar 'yan sandan NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

To sai dai kuma ci gaba a cikin kamen tsohon gwamnan ya fara tada hankalin 'yan adawa inda masu gwagwarmayar neman karbe iko na kasar ke zargin ana shirin kare su.

Tun kafin kame el Rufa'in dama samame a gidansa, shi ma tsohon ministan shari'a na kasar kuma jigo a Jam'iyyar ADC Abubakar Malami ya fuskanci salo iri guda da Rufa'in a hannun jami'an tsaron taraýyar Najeriyar.

Can cikin gidan adawar dai, yanzu haka ana ta nuna damuwa bisa dauki dai dai kan jiga jigan adwar da kila ma tasirin da yake shirin yi a kokarin karbar mulkin.

Karin BayaniKaduna: Martani kan binciken El-Rufa'i

Tsama cikin gidan na siyasa, ko kuma kokarin amsa laifi, ana ta'azarar kai kawon ne shekara guda da babban zaben da ke shirin gudana a tarayyar Najeriyar. Zaben kuma da tuni ya fara nuna alamun zafi a tsakanin magoya bayan APC yar mulki da yan uwansu na ADC da ke zaman mafi tasiri cikin gidan adawar yanzu haka.

Karin Bayani:El-Rufai na shirin yamutsa hazon siyasar Najeriya a 2027

Motar 'yan sanda cikin shirin tsaro
Motar 'yan sanda cikin shirin tsaroHoto: Nuhu Gwamna/REUTERS

Zubair Abdura'uf dai jigo ne cikin gidan APC yar mulki a Kaduna kuma a fadar sa abun da ke faruwa ga el Rufa'in na kama da karatun gwanon da ya fara sunsuna warin jikinsa.

Kai wa ya zuwa wanke allo, ko kuma kokarin aiken tsoro cikin gidan adawa, daga dukkan alamu ana kara matsawa ya zuwa babban zaben da faduwar gaba a bangaren adawar.

Isa Sunusi shugaban kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakki n 'yan Adam a kasar, ya ce ana bukatar sauyi cikin rawar siyasar Najeriyar a halin yanzu.

Masu mulkin kasar dai na tsakanin murde wuya cikin gidan adawar tare da aiken sako da ke da munin gaske, tare da barin adawar cikin barazanar rasa mulki.