Muhammadu Buhari ya karbi ragamar jagorancin Najeriya bayan da ya lashe zaben shugaban kasa a shakara ta 2015 karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Gabannin shigarsa siyasa, Buhari ya taba yin mulki soja . Daga cikin abubuwan da aka sanshi da shi su ne yaki da cin hanci. An dai haifi Buhari ne a shekara ta 1942 kuma mutumin jihar Katsina ne a arewa maso yammacin Najeriya