Najeriya na ci gaba da shiga matsaloli | Siyasa | DW | 06.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya na ci gaba da shiga matsaloli

Baya ga mummunar matsalar tsaro da ke addabar Najeriya, akwai tarin matsaloli kama daga na dinbin rashin aikin yi da kuma talauci da ya yi wa al'umma katutu. An kuma samu rade-radi na juyin mulki.

Karikatur: Nigeria Banditen

Matsaloli sun gaza kare wa a Najeriya

Matasalar tsaro na kara ta'azzara a Tarayyar ta Najeriya, inda a yanzu ana iya cewa babu wani yanki da ya tsira daga barazanar tsaron. Kama daga 'yan ta'addan Boko Haram da ke yankin Arewa maso Gabas, zuwa ga 'yan bindiga da masu garkuwa da suka yi kaka gida a yankin Arewa maso Yamma da ma Arewa ta Tsakiya.

Wasu daga cikin karin matsalolin da al'ummar Najeriyar ke fama da su sun hadar da dinbin talauci da yunwa da kuma rashin aikin yi da ma rashin wadatattun hanyoyin kula da lafiyar al'umma. Wadannan abubuwa dai masana na ganin suna da alaka wajen karuwar ayyukan na ta'addanci da ya yiwa kasar katutu.

 A hannu guda kuma, gwamnatin kasar ta yi zargin cewa wasu na shirya makarkashiyar kifar da gwamnati ta hanyar juyin mulki, zargin kuma da jam'iyyar adawa ta PDP da ma kungiyoyin shiyyoyin kasar suka bayyana da kokarin dauke hankulan al'umma daga irin gazawar da gwamnati ta yi na kare musu rayuka da dukiyoyinsu.

DW.COM