APC jam'iyya ce ta Najeriya wadda ta hada wasu jam'iyyu daga bangaren adawa, kafin zaben shekara ta 2015, kuma jam'iyyar ta yi nasara a wannan zaben.
Jam'iyyar APC ta yi gagarumin adawa da mulkin PDP kafin zaben shekara ta 2015 musamman kan fannonin tsaro da tattalin arziki da zamantakewa. APC ta samu gagarumin nasara yayin zaben shekara ta 2015 da aka yi a Najeriya.