Fashola dan siyasa ne a kudancin Najeriya wanda ya yi gwamna jihar Legas da ke zaman cibiyar kasuwanci a Najeriya.
Lagas ta samu ci gaba mai ma'ana a shekaru 8 din da ya yi a matsayin gwamna wato daga 2007 zuwa 2015. Bayan da ya bar mukamin gwamna an nada shi minista a gwamnatin Muhammadu Buhari a shekarar 2015.