Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
EFCC hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya.
Hukumar tana yaki da zamba gami da masu handama da babakere da duniyar gwamnati a Najeriya. A shekara ta 2003 aka kafa hukumar.
Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya goyi bayan matakin canja takardun Naira don yaki da halarta kudin haram a Najeriya.
Hadin gwiwar hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma sun gana a birnin Yamai inda suka yi don duba matsalar a cikin kasashen yankin da ma nazarin yadda za a hada karfafa musayar bayanai.
Shirin ya kunshi labarai da rahotanni daga sassan duniya har ya zuwa halin da ake ciki a zaben rabin wa'adi na Amirka da kuma shirin Abu Namu da Darasin Rayuwa.
Babbar kotu da ke Abuja ta nemi a tasa keyar shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa zuwa gidan yari saboda kin bin umurnin kotu, lamarin da ya haifar da martani mai zafi a kan wannan batu da ya zama ba sabon ba.
A ci gaba da kokari na tona asirin masu cin hanci da rashawa a Najeriya, an kadammar da wata sabuwar manhaja da za ta bayar da dama ga ‘yan kasar su yi tonon silili ga masu aikata wannan mumunan dabi’a.
Jami'an hukumar EFCC a Najeriya, sun kama tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha a gidansa da ke birnin Abuja. An dai kwashe lokaci kafin jami'an suka kai ga kama shi.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC ta cafke babban Akanta na kasar bisa zargin kwashe Naira biliyan 80 a kamen da ba saba ganin irin sa ba.
Hukuncin daurin shekaru takwas da wata kotun ta yi wa tsohon shugaban hukumar fansho ta Najeriya Abdulrasheed Maina bayan samun sa da laifin satar kudin fansho Naira bilyan biyu ya sanya martani
Cikin shirin za a ji a Najeriya hukumar EFCC ta kadammar da wata sabuwar manhaja da zata bai wa alumma damar fallasa masu aikata laifufuka na cin hanci da rashawa. A Nijar matasan Agadez ne ke farin ciki bayan da kasar Aljeriya ta bude iyakarta bayan rufe ta da ta yi a bara saboda corona.
A cikin shirin za ku ji yadda shugaban hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci a Najeriya ke zargin ana kokarin lahanta masa rayuwa. Akwai rahoto kan yunkurin gwamnatin Nijar na gyara alaka da 'yan jarida. Sai kuma shirin Tushen Afirka da Taba Ka Lashe.
A Najeriya shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar da nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasar, wato EFCC.
A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji kwamitin binciken tsohon shugaban hukumar EFCC a Najeriya ya bukaci da kar a sake ba dan sanda damar jagorantar hukumar. A Nijar kuma kungiyoyin fararen hula na son 'yan siyasa su hau teburin sulhu don guje wa tarzomar zabe.
Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa domin yin nazari dangane da zargin cin hanci a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasar wato EFCC, ya mika rahotonsa.