1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan ranakkun zabe a Najeriya

Uwais Abubakar Idris
February 16, 2026

Korafe-korafe sun mamaye ranakkun yin zaben 2027 da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta INEC ta sanar.

https://p.dw.com/p/58qpg
Nigeria Wahlen 2023
Hoto: Benson Ibeabuchi/AFP

A Najeriya wata takaddama na can ta kaure biyo bayan sanar da ranakkun da za'a gudanar da zabubbukan gama gari na shekarar 2027, wanda suka fado a dai dai lokacin da al'ummar musulmi ke gudanar da azumin watan Ramadan. Abinda ya sanya nuna damuwa da kiran hukumar zaben kasar INEC ta sauya lokacin domin zai shafi yanayin fitowar jama'a don yin zaben da ke da muhimmanci a kasar.

Nigeria Wahlen 2023
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Karin bayani: Shin jadawalin zaben Najeriya na shekara ta 2027 zai yi aiki?

 Kama daga jam'iyyun adawa ya zuwa malaman addinai da ma sauran ‘yan Najeriya na ci gaba da korafi kan ranakkun da aka ayyana. Suna nuna damuwa lallai sai hukumar ta yi nazari tare da sake in dai don jama'a ake yi. Wannan ya biyo bayan sanya ranakkun zaben da ya yi karo da lokacin da al'ummar musulmai za su kasance suna azumin watan Ramadan a shekarar ta 2017.

Tuni aka tsayar da ranakkun zaben na 2027

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta ADC ce kan gaba a kan wannan, baya ga majalisar koli ta addinin Islama. Sanarwar da hukumar zaben Najeriyar ta yi, ya nuna cewa za'a yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya a ranar 20 ga watan Febrairun 2027, yayin da na gwamnoni kuma zai biyo baya a ranar 6 ga watan Maris.

Duka wadannan ranakku sun fado cikin azumin watan Ramadan ne wanda za'a fara daga ranar 7 ga watan Febrairu zuwa 8 ga watan Maris na shekarar ta 2007.

Nigeria | Wahl
Hoto: Christopher Onah/Focal Point Agency/IMAGO

Matsayin INEC kan kiraye kirayen jama'a

Tuni dai masu korafe-korafen suka aike wa hukumar zaben Najeriya sanin cewa ta sha dage zabubbuka a kasar bisa dalilai mabambanta, wasu daga ciki na gazawar samar da kayan zaben kansu. Ko me hukumar zaben ke yi a yanzu a kan wannan batu?

Karin bayani: Najeriya: Ko INEC za ta gudanar da sahihin zabe a 2027?

Tsarin mulkin Najeriyar ya samar da lokaci mai tsawo na gudanar da zaben bai dage a kan wata rana guda da ba za'a iya canza ta ba, domin sashi na 135 na tsarin mulkin na 1999 ya samar da tanadi ne na a gudanar da zaben kafin kwanaki 30 na cikar wa'adin mulki watau 29 ga watan Mayu kenan.