INEC hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wadda aka kafa lokacin da sojoji suke shirin mayar da Najeriya tafarkin demokaradiyya.
Hukumar ta fara shirya zabuka na kasa baki daya tun shekarar 1998, amma daga bisani an mayar da zabukan kananan hukumi karkashin gwamnatocin jihohi, inda suke kula da zaben kananan hukumomi, yayin da INEC ke shirya zabuka na majalisun jihohi da gwamnoni da 'yan majalisa na tarayya gami da shugaban kasa.