CDU ko Christian Democratic Union guda ce daga cikin manyan jam'iyyun da ke Tarayyar Jamus.
CDU ita ce jam'iyyar da ta fi kowacce jam'iyya samun dama wajen jagorantar Jamus daga lokacin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu. Angela Merkel da ke cikin jerin wanda suka shugabanci Jamus na daya daga cikin fitattun 'ya'yan jam'iyyar.