1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 26, 2024

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sha alwashin tsaurara dokokin amfani da wuka, tare da hanzarta aiwatar da shirin mayar da masu neman mafakar siyasa da ba a amince da takardunsu ba zuwa kasashensu na asali.

https://p.dw.com/p/4jwXC
Kwafi mahada
Deutschland Solingen | Olaf Scholz gedenkt den Opfern des Messerangriffs
Hoto: Henning Kaiser/REUTERS

Shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ya bayyana matsayar gwamnatin sa kan wannan harin, yayin da ya shiga sawun wadanda ke ajiye furanni a wajen da aka kai harin a garin na Solengen domin tunawa da kuma girmama wadanda suka halaka. A cewarsa ransa ya baci matuka kan wannan harin da ya jikkata karin mutane takwas bayan ukun da suka halaka. Sholz ya bayyana cewa tilas ne su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ganin ba a ci gaba da samun wadannan hare-hare a kasar ba, inda ya ce:

"Wannan ta'addanci ne, ta'addanci gare mu baki daya da kuma ke barazana ga rayuwarmu da dorewar dangantakarmu da yadda muke gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum. Wanna kuma shi ne burin wadanda ke tsarawa da kai irin wadannan hare-haren a koda yaushe, abin da kuma ba za mu taba amincewa da shi ba ke nan."

Karin Bayani: Scholz zai ziyarci garin da aka kashe mutane uku a Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz yayin alhinin harin ta'addanci da wuka
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz yayin alhinin harin ta'addanci da wukaHoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images

Sholz ya kara da cewa, kasa daya ce al'umma daya kuma gwamnati ba za bari wasu su zo su tarwatsa ta ba ta hanyar aikata munanan ayyuka da ta'addanci. A cewarsa za su dauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da ganin an cafke tare da hukunta wadanda ke da hannu a wannan ta'addancin yana mai cewa: 

"Na yi magana kan yadda raina ya yi matukar baci, bacin raina a kan 'yan IS ne saboda dorewar zaman lafiyarmu baki daya. Koda ace barazanarsu a kan Yahudawa take ko Kiristoci da Musulmi, mu din kasa daya ce al'umma daya kuma ba za mu bari su tarwatsa mu ba."

Masu fashin baki dai na ganin harin na Yammacin Jamus ka iya kara karfi ga jam'iyyar AfD ta masu matsanancin ra'ayin kyamar baki da ta jima tana yin kira da a sake dokoki da tsari a kan baki a Jamus din musamman a yankin gabashin kasar. Kana harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a jihohi biyu na gabashin Jamus din, inda al'umma a jihar Saxony da kuma Thuringia za su kada kuri'unsu a ranar daya ga watan Satumbar da ke tafe.

Karin Bayani: Ana farautar mutumin da ya daba wa Jamusawa wuka Solingen

Jama'a na alhinin harin Solingen
Jama'a na alhinin harin Solingen Hoto: Thomas Banneyer/dpa/picture alliance

Ita ma dai jam'iyyar adawa ta CDU da ke cikin gwamnatin hadakar Jamus ta yi kakkausan suka a kan batun bakin masu neman mafaka, inda jim kadan bayan harin na Solingen cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Das Erste ko kuma ARD na Jamus din shugaban jam'iyyar ta CDU Friedrich Merz ya bukaci gwamnatin Scholz da ta hanzarta mayar da 'yan gudun hijira kasashensu na asali. Ya kara da cewa ba za a sake amincewa da masu neman mafaka daga Afghanistan da Siriya ba, kuma duk wanda ya samu mafaka a Jamus daga wadannan kasashen sannan ya ziyarci kasarsa ta asali to ya rasa takardunsa ke nan.

Sai dai tuni sakatare janar na jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnati Olaf Scholz da ke mulki Kevin Kühnert ya sa kafa ya yi fatali da bukatar ta Merz yana mai cewa da yawa cikin kalamansa sun saba da dokokin neman mafaka:

"A fannin mayar da masu neman mafakar da aka yi watsai da takardunsu, gwamnati na aiki domin samar da mafita a kan 'yan Siriya da Afghansitan. Muna kuma aiki tare wajen ganin an samar da dokokin amfani da bindiga da haramta wukake, aiki ne na masu tsattsauran ra'ayi matasa da suke yi domin radin kansu. Tilas mu yi aiki a kan yadda tsattsauran ra'ayi ke samun karbuwa, kuma muna da kwararru a wannan fanni cikin al'ummarmu." 

Karin Bayani: Shekaru 20 bayan kisan baki a garin Solingen

Tun da fari da yake mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, Scholz cewa ya yi:

Taron alhinin mutanen da aka kashe a hari da wuka a Solingen
Taron alhinin mutanen da aka kashe a hari da wuka a SolingenHoto: Henning Kaiser/dpa/picture alliance

"Bari in fara da bayyana wani abu a kan dangin wadanda aka halaka, muna masu alhinin kisan su. Muna masu addu'a ga iyalan wadanda suka samu raunuka, za kuma mu ci gaba da yi duk da cewa mun samu labari mai dadi na cewa da yawa daga cikinsu sun fita daga cikin yanayi na hadari."

A cewarsa suna aiki tukuru domin gaggauta fara aiki da dokar mayar da masu neman mafakar da ba su samu takardu ba zuwa kasashensu na asali tare da majalisar dokokin Jamus ta Bundestag da kuma takwararta ta jihohi wato Bundesrat.

Tuni dai wanda ake zargi da kai harin ya mika kansa ga jami'an 'yan sanda, kwana guda bayan lamarin ya afku a lokacin bikin cikar birnin na Solengel da ke jihar North Rhine-Westphalia shekaru 650 da kafuwa. Masu shigar da kara na gwamnatin Tarayya sun bayyana cewa, mutumin na da tsattsauran ra'ayi irin na 'yan ta'addar IS da ba su kai ga sanin lokacin da ya shiga kungiyar ba. Mai shekaru 26 a duniya, matashin na cikin masu neman mafakar da ba a amince da takardunsu ba da kuma aka shirya mayar da shi zuwa Bulgariya a bara karkashin dokokin kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU na mayar da masu neman mafaka kasar da suka fara shiga amma kuma ya yi batan dabo.