Berlin shi ne babban birnin tarayyar Jamus. Birnin na daga cikin biranen kasar da ke da yawan jama'a.
Birnin Berlin yana yanki ne na gabashin Jamus kuma tun cikin shekara ta 1990 aka maida shi babban birnin Tarayyar Jamus. Birnin dai ya zama wata alama ta rarrabuwa da sake hadewar Jamus kuma waje ne da masu yawon bude idanu kan ziyarta sosai.