Merkel ta yaba da taimakon Hungary | Labarai | DW | 17.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yaba da taimakon Hungary

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta jinjina wa gwamnatin kasar Hungary, kan rawar da ta taka a gabanin sake hadewar kasashen Jamus biyu.

Angela Merkel ta ce, matakin Hungary na bude kofofinta ga dubban 'yan kasar tsohuwar Jamus ta Gabas da rikicin ya tagayyara, ya ceci rayukansu tare da ba su damar shiga gwagwarmayar fafutukar faduwar katangar Berlin da ta haramta shige da fice. 

Merkel ta ce karamcin ya taka muhinmiyar rawa a nasarar da aka samu a hadin kan da ya samu a shekarar 1990 a tsakanin yankin Yammanci da Gabashin kasar Jamus.

A na sa ran Shugabar gwamnatin, za ta kai wata ziyara kasar ta Hungary a ranar Litinin mai zuwa, inda za ta gana da Firai ministan kasar Victor Orban, ziyarar ita ce ta farko tun bayan tsamin dangantaka a tsakanin shugabanin biyu, kan batun 'yan gudun hijira a shekarar 2014.