Shugabannin kasashen Afirka za su gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran kusoshin gwamnati da 'yan kasuwa a birnin Berlin domin yin waiwaye kan tasirin yarjejeniyar habaka tattalin arzikin Afirka.
Manufar taron shi ne maida hankali kan yadda za a jawo hankalin masu hannu da shuni daga kasashen masu arziki domin zuba jari a nahiyar Afirka.
Shekaru uku kenan da gwamnatin Jamus ta kirkiro da tsarin kulla yarjejeniyar kawancen bunkawa tattalin arzikin kasashen Afirka "Compact with Afrika" inda ma'aikatar raya kasashe na Jamus ta fara yarjejeniyar da kasashen Tunisia da Ghana da Ivory Coast.
A shekarar 2019 ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Müller zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejniya da kasashen Moroko da Senegal da kuma Habasha.