Kungiyar G20 ta kunshi kasashen duniya da ke kan gaba wajen harkoki na tattalin arziki. Shugabannin kungiyar kan yi taro sau biyu a kowacce shekara.
Kimanin kashi 80 cikin 100 na harkokin kasuwanci a duniya na faruwa ne a kasashen da ke cikin kungiyar. Galibin kasashen dai sun fito ne daga Turai da Asiya da Amirka. A shekara ta 2009 ne aka kafa kungiyar don maye gurbin kungiyar kasashen G8.