Rarrabuwar kawuna a taron G20 | Labarai | DW | 02.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rarrabuwar kawuna a taron G20

Ministocin harkokin waje na kasashe masu arzikin masana'ntu na shirin ganawa a yau a birnin New Delhi na Indiya a cikin rarrabuwar kawunan kan yakin Ukraine.

Tuni da jagoran diflomasiyyar Amirka Antony Blinken da ake sa ran zai halarci taron,ya yi gargadin cewar ba zai gana ba da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a wannan ganawar ta kwanaki biyu tsakanin ministocin harkokin wajen na G20. A ranar Asabar, taron ministocin kudi na G20 an waste hannun riga saboda China da Rasha sun ki amincewa su saka hannu a kan sanarwar bai daya ta karshen taron.