Kofin Duniya na hukumar kwallon kafa wato FIFA 2018 wanda Rasha ke karban bakoncinsa daga 14.06.2018 zuwa 15.07.2018 wanda kasashe 32 ke halartan gasar ta 21 a wasanni mafi girma na cin kofin kwallon kafan duniya.
An bai wa Rasha izin karban bakwancin gasar cin kofin duniya a 2018 bayan kada kuri'a da wakilan FIFA suka yi a shekara ta 2010 wanda a wannan taron aka bai wa Katar izinin daukan nayin gasar ta cin kofin kwallon kafan duniya na 2022.