1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kofin Duniya: Maroko ta doke Beljiyum

November 27, 2022

Wannan dai shi ne karo na farko da Maroko ta iya zura kwallo a gasar cin kofin duniya a cikin shekaru 24 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4K9rm
'Yan wasan Beljiyum na neman kwatar kwallo a hannun dan wasan Maroko
'Yan wasan Beljiyum na neman kwatar kwallo a hannun dan wasan MarokoHoto: Fadel Senna/AFP/Getty Images

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya, a wannan Lahadi, Maroko ta lallasa kasar Beljiyum da 2-0. 'Yan wasan Beljiyum wadanda suka zo na uku a gasar cin kofin duniya ta 2018 tun da farko sun so samun galaba a wannan wasa na yau da zai ba su damar zuwa mataki na gaba a rukunin F. To amma 'yan wasan Moroko  Abdelhamid Sabiri da Zakaria Aboukhlal sun katse wa  Beljium hanzari ta hanyar zura wa Turawan na Beljiyum kwallaye biyu a raga ana dab da tashi wasa.