1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Merkel ta fara wa'adi na hudu

Mohammad Nasiru Awal USU | Lateefa Mustapha Ja'afar
March 14, 2018

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta tabbatar da Angela Merkel a mukamin shugabar gwamnatin Jamus karo na hudu a jere. Cikin abubuwa da ke gaban gwamnati har da batun alaka da Afirka da zuba jari.

https://p.dw.com/p/2uIFp
Deutschland Bundestag Kanzlerwahl
Hoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

An dai rantsar da sabuwar gwamnatin hadakar karkashin jagorancin Shugabar gwamnati Angela Merkel ta jam'iyyar CDU a wannan Laraba bayan da aka yi zabe cikin watan Satumbar bara ba tare da samun rinjayen da zai bai wa jam'iyyar Merkel din damar kafa gwamnati ita kadai ba. Tun dai a shekarar da ta gabata ne gwamnatin Jamus din ta fara mayar da hankali sosai a kan nahiyar Afirkan da take wa kallon mai matukar muhimmanci gareta. A karkashin yarjejeniyar kafa gawamnatin hadakar dai, an yi batu kan Afirka har sau 28, abin da ke zama wani ci gaba ga nahiyar da a baya Jamus din ba ta damu da lamuranta ba. A yayin taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya wato G20, Jamus ta sanar da daukar wasu matakai guda biyu na hada kai da kasashen Afirkan na farko shi ne shirin kasashen 20 masu karfin tattalin arziki na G20 na bunkasa harkokin zuba jari da kuma samar da kayayyakin more rayuwa. Duk da cewa kawo yanzu ba a samu wani abun azo a gani ba dangane da wadannan matakai guda biyu, yarjejeniyar kafa gwamnatin hadakar ta nunar da cewa Jamus ta dauki Afirka da muhimmanci a cewar Frank Heinrich wakili a majalisar dokoki daga jam’iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel kana masani a kan nahiyar Afirka, yana mai cewa:


"Tuni aka fara daukar matakai. Tun a bara da kuma bara waccan muka yi sauyi a kason da muke bayar wa ga Afirka, wannan na zaman matakin farko tun ma kafin a cimma yarjejeniyar."

Deutschland G20 Afrika Treffen
Merkel ta gana da shugabanni da dama na Afirka a taron G20 a baraHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Sohn

Gwamnatin hadakar wadda jam’iyyun da ke cikinta basu sauya ba, ta samar da sabuwar doka ta masu zuba jari domin taimaka wa masu kananan da matsakaitan sana’o’i su zuba jari a Afirka, kana za a rage hadarin da kamfanonin ka iya fuskanta ta hanyar wani tsari na bayar da garanti da zai bayar da kariya ga kamfanonin Jamus misali idan wadanda suka ci bashinsu a kasashen ketare sun gaza biya. Gwamnatin na kuma tunanin yin gyara a fannin bayar da agaji kamar yadda Angela Merkel ta sanar. A hirarsa da tashar DW Daraktan cibiyar Arnold-Bergstraesser da ke birnin Freiburg a Jamus Andreas Mehler kana kwararre a kan Afirka, ya nunar da cewa idan aka yi la'akari da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadakar da aka cimma a baya, za a ga cewa an fi yin batu a kan Afirka a wannan sabuwar yarjejeniyar. Sai dai game da batun zuba jari Mehler ya nunar da cewa: 

"Zan iya cewa zai yi wahala masu zuba jari daga Jamus su yi tururuwa zuwa Afirka fiye da a baya, kasancewar babu damarmakin kasuwanci masu yawa. Jamus na son kai kayayyakin fasaha zuwa Afirka wadanda kuma mafi akasari ba a bukatarsu a Afirkan."

Kungiyoyi masu zaman kansu da ma jam’iyyar masu rajin kare muhalli ta The Greens, na yin taka tsan-tsan kan yarjejeniyar. Ministan raya kasashe na Jamus Gerd Müller wanda shi ne ya sanya hannu kan shirin taimaka wa kasashen Afirka na Marshall Plan, ya nunar da cewa shirin ne zai zama abu na farko da sabuwar gwamnatin hadakar za ta fi mayar da hankali a kansa, ta hanyar koyar da kanana da matsakaitan sana’o’i. Gwamnatin ta Jamus dai na son ta mayar da hankali sosai a yammacin Afirka da kuma yankin Sahel da ke fuskantar matsalar tsageru masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama, da masu yin muggan ayyuka da suka hadar da safarar mutane zuwa Turai.