An haifi Angela Merkel a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 1954. A cikin shekara ta 2005 ce aka zabeta a matsayin shugabar gwamnatin tarayyar Jamus.
Merkel ta samu wannan matsayi na shugabar gwamnati ne karkashin tutar jam'iyyarta ta Christian Democrat (CDU) wadda ke da ra'ayin mazan jiya.