Manyan kasashen duniya na taronsu na koli | Labarai | DW | 19.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manyan kasashen duniya na taronsu na koli

Jamus ta bude sabon babin kyautata dangantaka tsakanin Turai da Amirka, daidai lokacin da sabon shugaban Amirka, Joe Biden, ya yi bayyanarsa farko.

Shugabar gwamnatin ta Jamus, Angela Merkel, ta bayyana hakan ne ga shugabannin da ke halartar babban taro kan al'amuran tsaro a duniya da aka yi ta hanyar sadarwar Intanet.

Lokacin taron Shugaban Amirka Joe Biden, ya yi alkawarin dawo da alakar kasarsa da manyan kasashen na yamma.

Daga cikin batutuwan da shugabannin suka ce za su mai da hankali a kai sun hada da batun taimaka wa kananan kasashen duniya, wajen samar musu da alluran riga-kafin cutar corona da batun yaki da matsalolin sauyin yanayi.

An dai jima kokawa a kan yadda kasashen da ke karfin tattalin arziki suka mamaye kamfanonin sarrafa alluran riga-kafin corona, inda aka bar kasashe matalauta a baya, duk kuwa da kasancewar wannan annobar duniya ce baki daya ta shafa.