Birnin Munich shi ne hedikwatar jihar Bavariya da ke kudancin tarayyar Jamus. A Munich din ne kamfanin kera motoci na BMW ke da hedikwatarsa.
Birnin mai yawan mutane sama da miliyan guda na da karfin tattalin arziki. Ya yi fice saboda kungiyar nan ta kwallon kafa ta FC Bayern Munich da kuma kamfanin inshora din nan na Allianz. Da zarar an ambaci Munich a kan tuna al'adra nan ta bikin shan barasa wato ''Oktoberfest''.