Jamus: Ganawar Merkel da Macron | Labarai | DW | 29.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Ganawar Merkel da Macron

A wannan Litinin Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ke kai ziyara Jamus inda zai gana kai tsaye da Shugabar gwamnati Angela Merkel, ganawar ita ce ta farko tun bayan bullar annobar Coronavirus. 

Ana sa ran Shugabannin biyu za su mayar da hankali kan tattauna batutuwa da suka shafi zaben shugabancin kwamitin Kungiyar tarayyar Turai da barazanar dumamar yanayi gami da matsalar 'yan gudun hijira. 

An dai shirya wani taron cin abincin dare inda nan ake ganin za su tattauna batun dangantaka a tsakanin kasashen biyu da Amurka da Chaina da Turkiyya da kuma matsalolin tsaro a kasar Libya da yankin Sahel na yammancin Afirka. Wannan ziyarar na zuwa ne a gabanin babban taron Kungiyar Tarayyar Turai da za a yi a tsakiyar watan gobe da zummar samar da kudade don farfado da tattalin arzikin kasashen yankin da Coronavirus ta yi wa barna.