Kasar Faransa na daya daga cikin kasashen da ke fada a ji a nahiyar Turai kuma tana daya daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar nan ta EU.
Faransa na nan a yammacin Turai, babban birninta shi ne Paris. Kasar na daya daga cikin kasashe biyar da ke da kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Har wa yau kasar na cikin kungiyar tsaro ta NATO da kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki a duniya.