1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Merkel ta yi kiran hadin kan Turai

Abdullahi Tanko Bala LMJ
June 18, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da kudirori da manufofin Jamus na shugabancin karba-karba na majalisar Tarayyar Turai, wanda Jamus din za ta karbi jagoranci a watan Yuli mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3e0Sj
Kanzlerin Angela Merkel im Bundestag
Hoto: Reuters/A. Hilse

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce babban kalubale na gaggawa da ke gaban Tarayyar Turai shine batun annobar corona wadda ta hallaka mutane fiye da 100,000 a nahiyar Turai da ke fuskantar koma bayan tattalin mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu. A cewar Angela Merkel, akwai bukatar tarayyar turai ta yi amfani da annobar corona wajen gudanar da garanbawul. 

“Tace muna rayuwa a wani zamani wanda duk da annobar da ake ciki, yanayin yadda muke rayuwa da gudanar da harkoki yana fuskantar gagarumin sauyi da kalubale ta fuskoki biyu, sauyin yanayi wanda muke tunkara da matakan rage hayakin CO2 mai gurbata muhalli da kuma sabbin fasahohi da ke sauya yadda muke gudanar da ayyuka da kuma zaman tare. 

Deutscher Bundestag Plenum Sitzung in Berlin
Hoto: picture-alliance/Flashpic/J. Krick

Shugbar ta kuma nuna irin raunin Tarayyar Turai inda ta baiyana takaicin yadda kasashe daidaiku suka tunkari yaki da annobar corona maimakon matakin bai daya daga kungiyar Tarayyar Turai. Ta kara da jaddada kudirin habaka tattalin arzikin kasashen nahiyar a wa'adin shugabancin Jamus na majalisar zartarwar Tarayyar Turan.

“Bai kamata mu yi sakaci ko nuna halin ko in kula ba, wadanda basa son cigaban dimukuradiyya, tsagerun 'yan kungiyoyin kama karya suna jira ne kawai su ga wata dama ta matsalar tattalin arziki ta faru su yi amfani da ita wajen yada rashin kwanciyar hankali".

A waje guda kuma Merkel ta kara da cewa tarayyar Turai na fuskantar gagarumin sauyi ta fuskar sauyin yanayi da sabbin fasahohi na cigaban zamani wadanda suke sauya yanayin zamantakewar rayuwar al’umma. A saboda haka tace wajibi ne a karfafa sauye sauye masu inganci ta na mai kashedin cewa wadanda basa son cigaban dimukuradiyya suna amfani da siyasa wajen kassara yaki da annobar corona.

“Cikakken yancin sabbin fasahohin zamani baya nufi cewa mu raba dukkan abin da yake nahiyar turai, sai don mu sami damar yankewa kanmu shawarar bangaren da nahiyar turai ke bukatar tsayuwa da kafafunta da kuma yadda muke so mu aiwatar da manufofinmu misali kafa ingantaccen rumbun adana bayanan kayayyakin cigaban rayuwar al’umma. Muna fata a shugabancinmu za mu habaka wannan bangare.”

Außenminister Heiko Maas
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Schmitz

Shi ma da yake tsokaci a game da ko Jamus za ta yi wata sadaukarwa idan ta karbi shugabancin majalisar zartarwar Turan, ministan harkokin wajen kasar Heiko Maas yayi bayani da cewa:

“Ina tsammanin Jamus bata bukatar yin wata sadaukarwa, to amma tarayyar turai tana da muhimmanci ga Jamus. A matsayinta na babbar kasa da ke fitar da haja zuwa kasashen waje, Jamus tana amfana da kasancewar nahiyar turai na bunkasa. Shi yasa muke so mu tabbatar da cewa kasashen da annobar corona ta yi wa mummunan ta’adi kamar Italiya da Spain sun sami kubuta daga annobar cikin gaggawa.

Jamus dai na fatan samun nasarar cigaban tattalin arziki da samar da kyakkyawar makoma ga tarayyar turai tare da fatan nahiyar za ta kasance mai dogaro da kanta wajen fasahar kere kere da kuma sabbin fasahohi na cigaban zamani.