FDP (Free Democratic Party, Free Democrats) jam'iyya ce da ta shafe tsawon lokaci tana kawance da jam'iyyar CDU a tarayyar Jamus.
A cikin shekara ta 1945 ne aka kafa jam'iyyar FDP. Jam'iyyar na da sassaucin ra'ayi kuma ta yi fice wajen rajin sama wa mutane 'yanci. A lokuta da dama an yi kawance da jam'iyyar wajen kafa gwamnati a Jamus. Masu adawa da jam'iyyar na mata kallon jam'iyyar 'yan birni ko kuma masu hannu da shuni.