An cimma matsayar kafa gwamantin hadaka a Jamus | Labarai | DW | 24.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma matsayar kafa gwamantin hadaka a Jamus

Jam'iyyun SPD da FDP da The Greens sun cimma matsayar kafa sabuwar gwamnatin hadaka a Jamus, watanni biyu bayan gudanar da zaben 'yan majalisa ta Bundestag.

Wannan nasara da aka samu na nufin cewar Jamus za ta kai ga samar da gwamnati ta gaba kafin kirsimeti, tsakanin masu ra'jin kare muhalli da masu kwarya-kwaryar manufar gurguzu da masu rajin habaka kasuwanci. 

Jam'iyyun uku na fatan majalisar Bundestag ta zabi Olaf Scholz na SPD a matsayin sabon shugaban gwamnati zuwa farkon watan gobe, wanda zai kawo karshen mulkin Angela Merkel na shekaru 16. Sai dai kawayen uku na fatan yi wa manaima labarai bayani kan inda suka dosa bayan sun yi zama na karshe a wannan laraba.

Wannan sabuwar gwamnati za ta kafa tarihin zama ta hadin gambiza da ta kunshi jam'iyyun uku, wacce kuma aka samar bayan kwanaki 73 na tattaunawa bayan gudanar da zabe