Jamus: The Greens ta amince da shirin kafa gwamnati | Labarai | DW | 06.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: The Greens ta amince da shirin kafa gwamnati

Jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli ta amince da shirin kafa gwamatin kawance na Jamus, kwana guda bayan da takwarorinta na SPD da FDP suka yi na'am da wannan yarjejeniyar.

Jam'iyya mai rajin kare muhalli a Jamus ta kada kuri'a a tsakanin mambobinta inda ta amince da yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnatin hadaka da sauran jam'iyu biyu da suka hada da SPD da FDP.

Wannan mataki na zama na karshe kafin majalisar dokoki ta Bundestag ta zabi Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus a hukumance a jibi Laraba. Tuni ma Olaf Scholz da ke jiran gado ya fidda jerin sunayen majalisar ministocinsa.

Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar Jamus da aka samu daidaiton jinsi a tsakanin ministoci 16 da ke zama maza 8 mata 8. Daga cikin matan da ke shirin karbar manyan mukamai, har da  Annalena Baerbock ta jam'iyyar The Greens wacce za ta kasance ministar harkokin wajen Jamus, sai Christine Lambrecht ministar shari'a ta yanzu da ke shirin zama ministar cikin gida.