Jamus: Tattauna yiwuwar kafa gwamnati | Siyasa | DW | 06.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus: Tattauna yiwuwar kafa gwamnati

Jam'iyyu biyu da manyan jam'iyyun Jamus na CDU/CSU da SPD ke zawarci don kafa gwamnatin hadaka, sun sanar da cewa za su fara tattaunawa da jam'iyyar SPD da ke kan gaba a zaben da ya gabata.

Babu dai tabbacin cewa za a cimma matsaya nan take a tattaunawa kan kafa gwamnatin hadakar da wadannan jam'iyyu za su yi. Jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli da ta zo ta uku a zaben, tafi karkata zuwa ra'ayin gurguzu yayin da FDP mai ra'ayin jari hujja da ta zo ta hudu a zaben na rana'ar 26 ga watan Satumbar da ya gabata, a baya-bayan nan ta karkata ga ra'ayin 'yan mazan jiya.

Sai dai in har suka cimma matsayar, hakan na nufin an kawo karshen gwamnatin jam'iyyar Angela Merkel ta CDU da abokiyar tagwaitakarta CSU da ke da ra'ayin 'yan mazan jiya, kuma hakan zai bai wa Olaf Scholz na jam'iyyar SPD wanda yanzu haka yake matsayin mataimakin shugabar gwamnati kana ministan kudi damar zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. A baya dai duka jam'iyyun sun yi tattaunawa ta tsakanin jam'iyyu biyu ne kawai, sai dai a yanzu jam'iyyun The Greens da FDP da kuma SPD sun sanar da cewa za su hadu su tattauna su uku kan batun na kafa gawamnati.

Da take jawabi kan tattaunawar tasu da ta yi wa jam'iyyar The Greens din takara wato Annalena Baerbock cewa ta yi:

Deutschland | Parteitag Bündnis90/Die Grünen

Annalena Baerbock ta jam'iyyar kare muhalli

"A 'yan kwanakin nan, mun tattauna da jam'iyyar CDU da abokiyar tagwaitakarta CSU kuma mun tattauna da SPD, ita ma FDP mun tattauna da ita. Duka tattaunawar ta yi armashi, kuma jam'iyyun sun yi kokarin tattauna bambance-bambancensu da kuma yadda za su shawo kansu domin cimma matsaya guda a mutumce. Bayan wadannan tatttaunawa mun tuntubi juna, inda muka amince da mu yi tattaunawa mai zurfi tare da jam'iyyun FDP da SPD musamman kan matsaya guda da muka yi nasarar samarwa a tsakaninmu cikin tattaunawwar da muka yi da kowaccensu. Wannan ita ce bukatar da muka mika ga FDP, domin mu hadu mu tattauna baki daya."

Tuni dai jagoran jam'iyyar ta FDP Christian Lindner ya bayyana cewa sun amsa wannan gayyata ta jam'iyar The Greens ta tattaunawa tare da jam'iyyar SPD ta masu ra'ayin gurguzu, sai dai ya ce babu batun irin wannan tattaunawar da hadakar jam'iyyun CDU da CSU a yanzu, yana mai cewa:

Sondierungsgespräche zwischen FDP & CDU

Christian Lindner na jam'iyyar FDP

"Jam'iyyar The Greens, ta bayar da shawarar mu yi tattaunawar farko ta hadin gwiwa da jkam'iyyar SPD. The Greens ta bayyana cewa har yanzu akwai yiwuwar su tattauna da tagwayen jam'iyyu na CDU/CSU domin kafa abin da ake kira da hadakar "Jamaica", kamar yadda kuma sani, muma hakan take gare mu. Mun amince da tattaunawar tsaknin jam'iyyu uku wato jam'iyyarmu da The Greens da kuma SPD ne, domin muga matsayar da za mu cimma domin ciyar da kasarmu gaba. Na yi wa Olaf Scholz tayin tattaunawa kamar yadda muka cimma yarjejeniya da The Greens, kan mu hadu a wannan Alhamis din. Za kuma mu tattaunawa din."

Sai dai a nasa bangaren dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus din Armin Laschet karkashin tagwayen jam'iyyu na CDU/CSU mai ra'ayin mazan jiya ta shugabar gwamnati Angela Merkel ya ce, har yanzu yana da sauran fata kan kafa gwamnati ta gaba, inda ya ce:

Nach der Bundestagswahl I Armin Laschet I CDU

Armin Laschet jagoran CDU

"Mataki na farko na kafa sabuwar gwamnatin Jamus ya bayyana kansa, tun ranar 26 ga watan Satumbar da ya gabata. Jam'iyarmu ce ta biyu a zaben, kuma a kwanakin baya-bayan nan mun tattauna da jam'iyyar FDP da kuma ta The Greens. FDP ta nuna alamun cewa akwai yarjejeniya da jam'iyyun CDU/CSU a wurare da daman gaske yayin tattaunawarmu da su. Mun sha bayyanawa karara cewa, jam'iyyun FDP da The Greens ne za su yanke hukunci kan mataki na gaba. Muna giramma tattaunawar da wadannan jam'iyyu biyu za su yi da SPD. Mun kuma nunar musu da cewa, a shirye muke mu kara zama kan teburin tattaunawar, hakan ce ta sa muke girmama ra'ayinsu. CDU da CSU a shirye suke domin tattaunawa."

Jam'iyyun biyu dai na The Greens da kuma FDP na iya hadewa da jam'iyyar ta SPD ko kuma ta CDU da abokiyar tagwaitakarta CSU domin samun rinjaye a majalisar dokokin Jamus din ta Bundestag, wanda hakan zai ba su damar kafa gwamnatin hadaka da za ta maye gurbin ta Angela Merkel.

  

Sauti da bidiyo akan labarin