Kafa gwamnatin hadaka a Jamus | Siyasa | DW | 24.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kafa gwamnatin hadaka a Jamus

Jam'iyyun SDP da Green da FDP a Jamus sun kammala tattaunawar kafa gwamnatin hadaka, domin kafa sabuwar gwamnatin da za ta canji Angela Merkel kafin bukukuwan Kirsimeti.

Koalitionsgespräche zwischen SPD, Grünen und FDP in Berlin

Hoton sabon kawancen da zai kafa sabuwar gwamnatin hadaka a Jamus

Jam'iyyun uku da ke kokarin kafa gwamnatin sun sanar da kammala tattaunawarsu ce a taron manema labarai da suka gudanar a wannan Laraba a birnin Berlin. Cimma yarjejeniyar ta zo ne bayan da wakilai 21 na jam'iyyun da suka hada da Social Democrats mai ra'ayin gurguzu da Jam'iyyar Green mai fafutukar kare muhalli da kuma jam'iyyar Free Democrats mai rajin cigaban kasuwanci suka gana tun da farko a wannan Laraba domin cimma matsaya.

Dan takarar shugaban gwamnati na Jam'iyyar SDP Olaf Scholz yace jam'iyyun uku sun cimma yarjejeniya ta kafa sabuwar gwamnatin hadaka wadda za ta maye gurbin gwamnati mai barin gado ta Angela Merkel kuma tattaunawar ta gudana cikin aminci da yarda da juna."Yace Jam'iyyun SPD da Green da FDP sun amince da kafa gwamnatin hadaka a tattaunawar da muka yi. Kuma za mu mika wannan yarjejeniya ga jam'iyyunmu domin su kada kuri'a akai. Muna fata dukkan jam'iyyun za su amince da wannan yarjejeniya cikin kwanaki goma masu zuwa."

Robert Habeck | Bundesvorsitzender von Bündnis 90/Die Grünen

Robert Habeck na jam'iyyar masu kare muhalli

A nasa bangaren wani babban jami'i na Jam'iyyar Greens Robert Habeck yace daidaita batun walwala da jin dadi al'umma tare da kare muhalli za su kasance ginshikai a manufofin sabuwar gwamnatin. "Yace za mu karbi jagorancin gwamnati a yanayi mawuyaci. To amma muna tabbatar da cewa za mu yi dukkan bakin iyawar mu domin mu dakile annobar Corona a karo na hudu."

Karin Bayani : Jamus ana tattauna yiwuwar kafa gwamnati

Shi ma shugaban jam'iyyar FDP Christian Lindner ya ce suna da kwakkwarar kudiri da fata mai yawa na ganin an sami sauyi mai ma'ana da cigaban zamani a Jamus. "Yace muna jin cewa akwai kudiri mai karfi na muradin chanji a kasar mu. wadannan Jam'iyyun uku basu boye komai ba a manufofinsu na ykain neman zabe a shekarun baya bayan nan. Muna nan akan bakar mu kuma za mu hada karfi wajen kawo sauyi na zamani musamman matasa sun bamu dama ta sauya yanayin da aka shiga a baya."

Deutschland Berlin | Sitzung Bundestag | Scholz und Merkel

Olaf Scholz da Angela Merkel

Majiyoyi sun ce jam'iyyun na fatan ganin majalisar dokoki ta Bundestag ta zabi Olaf Scholz a matsayin shugaban gwamnati a cikin mako na biyu na watan Disamba domin sabuwar gwamnatin ta fara aiki gadan-gadan. Makonni takwas da suka gabata ne dai a ranar 26 ga watan Satumba aka gudanar da zabe a nan Jamus, aka kuma fara tattauna kafa gwamnatin hadin gambiza a ranar 21 ga watan Oktoba.

Karin Bayani : Shirin kafa gwamnatin kawance a Jamus

Idan zaben Olaf Scholza matsayin shugaban gwamnati ya tafi kamar yadda aka tsara, zai kasance an dauki kwanaki 73 kenan kafin kafa sabuwar gwamnati bayan gudanar da zabe, sabanin zaben 2017 da aka dauki kwanaki 171 kafin a kai ga kafa gwamnatin hadaka tsakanin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma SPD.

Tattaunawar kafa gwamnatin kwancen a wannan karon ya sami nasarar warware matsaloli da dama tsakanin jam'iyyun Greens da FDP inda Greens mai rajin kare muhalli ta amince ta jingine bukatar takaita gudun ababen hawa a manyan hanyoyi yayin da FDP kuma ta amince za a za a habaka amfani da sabbin dabarun makamashi mara gurbata yanayi kamar iska da hasken rana sannan a dauki mataki sannu a hankali kafin a daina amfani da makamashin kwal a Jamus baki daya zuwa shekara ta 2030.